An yi adalci? - Shari'ar fyaɗe da aka kwashe shekara 32 ana tafkawa - BBC News Hausa (2024)

An yi adalci? - Shari'ar fyaɗe da aka kwashe shekara 32 ana tafkawa - BBC News Hausa (1)

Asalin hoton, Santosh Gupta

"A kullum zuciyata cike take da baƙin ciki. Nakan yi kuka na zubar da hawaye idan na tuna yadda lamarin ya wargaza min rayuwata."

A shekarar 1992. Sushma ta ce tana da shekara 18 lokacin da wani mutum, wanda ta sani ya ɗauke ta zuwa wani wurin ajiye kaya da ya daina amfani da shi, da nufin ana kallon fim a ciki.

A nan ne wasu maza shida zuwa bakwai suka kama ta suka kuma ɗaure ta tare da yi mata fyaɗe sannan suka ɗauki hotunan faruwar lamarin.

Mutanen dangin wani hamshaƙin attajiri ne mai ƙarfin faɗa a ji a birnin Ajmer, da ke jihar Rajastan a yammacin ƙasar.

"Bayan sun yi min fyaɗe, ɗaya daga cikinsu ya ba ni rufi 200 (dala biyu) don na sayi jan baki (kayan kwalliya), amma ban karɓi kuɗin ba,'' in ji ta.

A makon da ya gabata ne, shekara 32 bayan faruwar lamarin, wata kotu ta kama mutanen da laifi, sannan ta yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai.

"A yau ina da shekara 50, kuma ina ji a raina an yi mini adalci," in ji Sushma. "amma dai hukuncin ba zai sauya baƙin cikin da nake ji ba, sannan ba zai dawo min da kimata da na rasa ba."

Ta ce ta shafe tsawon shekaru tana fuskantar tsangwama da kyara daga mutane, saboda abin da ya faru da ita, kuma duk auren da ta yi a baya, idan mijin ya gano abin a ya faru da ita yakan sake ta.

Sushma na ɗaya daga cikin mata 16 - dukkansu ƴan makaranta a lokacin - da wasu mutane suka yi wa fyaɗe, suka kuma ɓata musu suna a wurare daban-daban a birnin Ajmer a shekarar 1992. Lamarin ya zama wata babbar badaƙala, sannan ya haifar da mummunar zanga-zanga.

A makon da ya gabata, kotu ta yanke wa mutum shida daga cikin 18 da ake zargi hukuncin ɗaurin rai da rai.

Ba su amince da aikata laifin ba, kuma lauyansu ya ce za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

An yi adalci? - Shari'ar fyaɗe da aka kwashe shekara 32 ana tafkawa - BBC News Hausa (2)

Asalin hoton, Santosh Gupta

To me ya faru da ragowar mutum 12 da ake zargin?

Takwas daga cikinsu an yake musu hukuncin ɗaurin rai da rai a 1998, to amma wata babbar kotu ta wanke huɗu daga ciki, yayin da aka sassauta hukuncin ragowar mutanen zuwa ɗaurin shekara 10.

Ga mutanen huɗu da aka wanke kuwa, ɗayansu ya kashe kansa, yayin da aka sake yanke wa wani hukuncin ɗaurin rai da rai a 2007, bayan shekara shida kuma aka wanke shi. An kuma kama ɗaya da ƙananan laif*cka kodayake daga baya an wanke shi, sai kuma ragowar ɗayan da har yanzu ake zargin ci gaba da ɓoye shari'arsa.

"Za ka iya kiran wannan da [hukuncin ranar 29 ga watan Agusta] adalci? Wannan hukunci babu adalci a cikinsa," in ji Santosh Gupta, wani ɗan jarida wanda ya yi rubuce-rubuce kan batun, ya kuma bayyana a matsayin shaida a kotu.

Haka ita ma wata lauya a ƙotun Kolin ƙasar Rebecca John, ba ta ji daɗin hukuncin ba, wanda ta kira da ''jinkirin adalci tamkar zalunci ne''.

"Wannan na nuna irin tarin matsalar da ɓangaren shari'armu ke fuskanta. Darajar al'ummarmu na zubewa, abin da muke fata shi ne ɗaukar matakin samar da gagarumin sauyi a fannin shari'ar ƙasarmu."

Mutanen da ake zargin kan yi amfani da ƙarfin faɗa-a-ji wajen yaudara da barazana da kuma danne mutanen da suka yi wa fyaɗen, in ji lauyan masu shigar da ƙara Virendra Singh Rathore.

Sukan ɗauki hotuna da bidiyon ƴan matan da suke yi wa fyaɗen, sannan su yi amfani da su wajen ɓata su a idon jama'a ko su yi wa wasu ƴan'uwan nasu fyaɗen, in ji shi.

"Akwai lokacin da suka gayyaci wani saurayi zuwa wani shagali sannan suka ba shi barasa ya yi mankas. Sai suka ɗauki hotunansa a lokacin da yake cikin maye, kuma suka yi masa barazanar wallafa hotunan a duniya idan bai kawo musu budurwarsa ba," in ji shi. "Da haka ne suke samun mutane da dama."

Mutanen da ake zargin na da alaƙa mai ƙarfi ta siyasa da dangantaka da manyan mutane. Wasu ma na da alaƙa da wurin bautar dargah (na mabiya addinin musulunci).

  • An samu tsohuwar hedimasta da laifin yi wa ɗalibai fyade

  • Mutumin da ya 'yi wa mai shekara 80 fyaɗe a Kano zai gurfana a kotu'

  • 'Mutum 12 sun yi wa 'yar shekara 12 fyade a Jigawa'

Mista Rathore ya ce an yi ta jan shari'ar ne tsawon shekara 32 sakamakon wasu dalilai, ciki har da rashin kama waɗanda ake zargin, da zargin jinkirta shari'ar daga lauyoyin waɗanda ake zargin, da rashin ɗaukar nauyin shigar da ƙarar, da kuma irin matsalolin da fannin shari'ar ke da su.

A lokacin da ƴansanda suka shigar da ƙara a 1992, ba a saurari ƙarar mutum shida daga cikin waɗanda ake zargin ba - sakamakon jingine ƙararsu da aka yi.

Mista Rahthore ya ce wannan kuskure ne, a lokacin da ƴansanda suka shigar da ƙara kan mutanen shida a 2002, ba su nan saboda sun gudu. An kama ɗaya daga cikinsu a 2003 sai mutum guda a 2005, sannan wasu biyu a 2012, yayin da aka kama na ƙarshen a 2018.

A duk lokacin da aka kama wanda ake zargin, sai a fara shari'ar a matsayin sabuwa.

"A ƙarƙashin doka, wanda ake zargi na da damar ya kasance a kotu a lokacin da shaidu ke gabatar da shidarsu, kuma lauyoyi na da damar yi musu tambayoyi kan shaidar da suke bayarwa," in ji Mista Rathore.

Hakan kuma na jefa mutanen da aka yi wa fyaɗen cikin firgici da tsangwama.

Mista Rathore ya tuna yadda wasu da aka yi wa fyaɗen, da a yanzu suke shekara 40 zuwa 50 suka riƙa kuka tare da kururuwa a gaban kotu, suna kokawa kan yadda ake gabatar da su a gaban kotu don bayar da hujja, shekara da shekaru bayan yi musu fyaɗe.

Yayin da lokaci ke shuɗewa, 'yansanda kan fuskanci cikas wajen bankaɗo shaidun.

"Da dama daga cikin wadanda aka yi wa fyaɗen a baya ba sa son alaƙanta su da matsalar, kasancewar sun manta da shi ," in ji Rathore.

Sushma - wadda ke ɗaya daga cikin mutum da gabatar da shari'arsu ta taka rawa wajen samun waɗanda ake zargin da laifi - ta ce ta riƙa magana a kafafen yaɗa labarai kan batun nata, saboda a cewarta ta san gaskiya take faɗa.

"Ban taɓa saura labarina ba. Lokaci da suka yi min laifin, ƙarama ce ni, ban san komai ba. Lamarin ya baƙanta min rai ya sa na rasa komai nawa, to kuma tsoron me zan ji, tunda na rasa komai,'' in ji shi.

Sushma : Mun sauya sunan domin kareta. Dokokin Indiya ba su bayar da dama a bayyana sunayen mutanen da aka yi wa fyaɗe ba.

An yi adalci? - Shari'ar fyaɗe da aka kwashe shekara 32 ana tafkawa - BBC News Hausa (2024)

References

Top Articles
Backpage Li
Fiddler'S Green - Tour 2024-2025
Spasa Parish
Rentals for rent in Maastricht
159R Bus Schedule Pdf
Sallisaw Bin Store
Black Adam Showtimes Near Maya Cinemas Delano
Espn Transfer Portal Basketball
Pollen Levels Richmond
11 Best Sites Like The Chive For Funny Pictures and Memes
Things to do in Wichita Falls on weekends 12-15 September
Craigslist Pets Huntsville Alabama
Paulette Goddard | American Actress, Modern Times, Charlie Chaplin
Red Dead Redemption 2 Legendary Fish Locations Guide (“A Fisher of Fish”)
What's the Difference Between Halal and Haram Meat & Food?
R/Skinwalker
Rugged Gentleman Barber Shop Martinsburg Wv
Jennifer Lenzini Leaving Ktiv
Justified - Streams, Episodenguide und News zur Serie
Epay. Medstarhealth.org
Olde Kegg Bar & Grill Portage Menu
Cubilabras
Half Inning In Which The Home Team Bats Crossword
Amazing Lash Bay Colony
Juego Friv Poki
Dirt Devil Ud70181 Parts Diagram
Truist Bank Open Saturday
Water Leaks in Your Car When It Rains? Common Causes & Fixes
What’s Closing at Disney World? A Complete Guide
New from Simply So Good - Cherry Apricot Slab Pie
Drys Pharmacy
Ohio State Football Wiki
Find Words Containing Specific Letters | WordFinder®
FirstLight Power to Acquire Leading Canadian Renewable Operator and Developer Hydromega Services Inc. - FirstLight
Webmail.unt.edu
2024-25 ITH Season Preview: USC Trojans
Metro By T Mobile Sign In
Restored Republic December 1 2022
12 30 Pacific Time
Jami Lafay Gofundme
Greenbrier Bunker Tour Coupon
No Compromise in Maneuverability and Effectiveness
Black Adam Showtimes Near Cinemark Texarkana 14
Ice Hockey Dboard
Über 60 Prozent Rabatt auf E-Bikes: Aldi reduziert sämtliche Pedelecs stark im Preis - nur noch für kurze Zeit
Wie blocke ich einen Bot aus Boardman/USA - sellerforum.de
Infinity Pool Showtimes Near Maya Cinemas Bakersfield
Dermpathdiagnostics Com Pay Invoice
How To Use Price Chopper Points At Quiktrip
Maria Butina Bikini
Busted Newspaper Zapata Tx
Latest Posts
Article information

Author: Madonna Wisozk

Last Updated:

Views: 6135

Rating: 4.8 / 5 (48 voted)

Reviews: 87% of readers found this page helpful

Author information

Name: Madonna Wisozk

Birthday: 2001-02-23

Address: 656 Gerhold Summit, Sidneyberg, FL 78179-2512

Phone: +6742282696652

Job: Customer Banking Liaison

Hobby: Flower arranging, Yo-yoing, Tai chi, Rowing, Macrame, Urban exploration, Knife making

Introduction: My name is Madonna Wisozk, I am a attractive, healthy, thoughtful, faithful, open, vivacious, zany person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.